• Wed. May 15th, 2024

Bana Azumi 30 Za’ayi A Watan Ramadan — Masana

ByEditor

Apr 3, 2024

Masana harkokin ilimin sararin samaniya sun ce bana azumin watan Ramadan 30 Za’ayi saboda bincike ya nuna cewa a ranar 29 ga watan baza a iya ganin sabon watan Shawwal ba.

Masanan sun bayyana cewa a ranar litinin 8 ga watan Afirilun 2024 wacce zata kasance 29 ga watan Ramadan, watan zai bayyana da misalin karfe 07:21 WAT wanda a wannan lokacin babu wanda zai iya ganin watan a duniya.

KU KARANTA: An Ga Watan Azumi a Nigeria — Sarkin Musulmi

Masanan sun ce sai a ranar Talata 9 ga watan Afirilun 2024 za’a iya ganin watan a Nahiyar Turai da Afirka da kuma Kasashen Nahiyar Amurka.

Masanan sun bayyana cewa a Nigeriya Azumin Ramadan 30 Za’ayi da mafi yawancin sassan Duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *