• Thu. May 16th, 2024

KAROTA Za Ta Girke Jami’anta 1,500 Don Kula Da Zirga-zirgar Ababen Hawa a Bukukuwan Sallah

ByEditor

Apr 8, 2024

Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA za ta zuba Jami’anta guda 1,500 domin sa ido a shagulgulan Bukukuwan Karamar Sallah.

Hukumar ta ce za ta zuba Jami’an ne domin su tabbatar da bin dokokin tuki a yayin shagulgulan Sallah.

Cikin wata sanarwa da Mai Magana da yawun hukumar Nabulisi Abubakar Kafar Na’isa ya aikowa GLOBAL TRACKER, hukumar ta ja hankalin jama’a da su kiyaye tare da bin doka sau da ķafa domin gujewa hadura a lokacin shagulgulan bikin Sallah.

KU KARANTA: KAROTA Ta Kama Motaci 4 Kirar J5 Makare Da Giya

Hukumar ta ce ta Haramta guje-guje da Ababen Hawa da wasu ke yi, wadanda hakan ke zama barazana ga rayuwar al’umma.

KAROTA ta ja hankalin iyaye da su guji bawa yaran da suke kasa da shekara 18 tuka abin Hawa, domin kuwa Hukumar ba za ta lamunta ba

A karshe, Hukumar ta yi fatan alkhairi ga jama’a tare da fatan kammala shagulgulan bikin Sallah lafiya.

Ta kuma umarci jami’anta da su kasance masu bin doka a lokacin ayyukan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *