• Wed. May 15th, 2024

Dan Majalisar Dokokin Kano, Ibrahim Kundila Ya Rasu

ByEditor

Apr 7, 2024

Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar kananan hukumomin Bagwai da Shanono Alhaji Halilu Ibrahim Kundila ya rasu.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa jaridar SOLACEBASE cewa dan majalisar wanda da ya raba kayan agaji ga al’ummar mazabarsa a makon jiya, ya rasu ne a gidansa da yammacin Asabar din nan.

KU KARANTA: Dan Majalisar Gwale Zai Dauki Nauyin Karatun Dalibai 501 a Kano ‘Polytechnic’

An gudanar da sallar jana’izar Alhaji Halilu Ibrahim Kundila dan jam’iyyar APC mai shekaru 59 a duniya a safiyar Lahadi a Kundila da ke karamar hukumar Shanono ta jihar Kano.

Daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar akwai dan majalisar wakilai mai wakiltar Shanono/Bagwai a Majalisar wakilai ta Kasa Honarabil Yusuf Ahmad Badau.

Marigayin mai shekaru 59, ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 17.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *