• Wed. May 15th, 2024

Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Kwamishino 4, Masu Bashi Shawara 8

ByEditor

Apr 18, 2024

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabbin kwamishinoni guda hudu (4) da masu bashi shawara na musamman guda takwas (8).

An gudanar da rantsuwar ne a Afrika House dake gidan gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya rantsar da mustapha Rabiu kwankwaso a matsayin kwamishinan matasa da wasanni da Abduljabbar Garko kwamishinan kasa da sabiyo da Shehu Aliyu Yar-medi kwamishinan ayyuka na musamman sai kuma Adamu Aliyu Kibiya kwamishinan kasuwanci da masana’antu.

KU KARANTA: Dan Takarar Shugabancin K/H Ungogo Ya Taya Gwamnan Kano Nasara a Kotun Koli

Gwamna Yusuf ya Kuma ja hankalinsu da su zama masu gaskiya da rikon Amana a dukkannin lamuransu na yau da kullum.

Haka kuma, gwamnan ya rantsar da masu bashi shawara wato “Special Advisers” su takwai 8.

Gwamnan ya horesu da su zama masu gaskiya da rikon Amana gami da Adalci a shugabancinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *