• Wed. May 15th, 2024

Fitacciyar Jarumar Kannywood Daso Ta Rasu

ByEditor

Apr 9, 2024

DAGA: SANI IDRIS MAI-WAYA, KANO

Fitacciyar Jarumar Masana’antar shirya fina-finan Hausa a Nigeriya dake da shalkwatarta a jihar Kano Hajiya Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso ta rasu.

Daya daga cikin daraktocin Masana’antar Ibrahim Bala ya shaidawa wakilin GLOBAL TRACKER cewa marigayiyar lafiyar ta lau har lokacin da ta yi sahun, duk da yake tana dan fama da mura.

Ya ce har da asubar yau ta yi sahun lafiya cikin walwala da jama’a a cikin iyalai da Yan uwa.

KU KARANTA: Jarumar Kannywood Bintu Ta Dadin Kowa Ta Rasu

Ko wanne lokaci daga yanzu ake sa ran yin jana’izarta, amma wata majiya ta ambato Jarumin Masana’antar Alhassan Kwalli na cewa za’a yi jana’izarta da misalin karfe 4 na yamma.

Saratu Gidado da ta fi fitowa a matsayin Uwa a cikin fina-finan Hausa wacce take da kafiya akan duk abinda ta yadda shine gaskiya a cikin fina-finan ta.

Akwai Karin bayani….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *