• Wed. May 15th, 2024

Kotu Ta Rusa Dakatarwar Da Hukumar Tace Fina-finan Kano Ta Yiwa Wasu Kamfanoni 3

ByEditor

Apr 12, 2024

Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin Mai shari’a Hadiza Suleiman ta rusa umarnin da hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jihar Kano ta yi na dakatar da ayyukan wasu kamfanoni uku daga gudanar da kasuwancinsu a Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Kannywood Enterprises LTD da Amart Entertainment, da Hajiya A’isha Tijjani yayin da wadanda ake karan su ne Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i Jihar Kano da shugaban hukumar Abba El-Mustapha.

Kotun ta kuma amince da bukatar da masu kara suka gabatar ta hannun lauyansu Barista AA Rabi’u Doka inda ya roki kotun ta soke duk wani hukunci ko umarni ga wadanda akayi kara suka yi kan masu kara a ranar 15 ga Fabrairu 2024.

KU KARANTA: Hisbah Ta Kama Fitacciyar Yar Tiktok Murja Kunya a Kano

Kotun ta kuma amince da bukatar masu karar uku da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na halal har zuwa lokacin da za a saurari karar da ke gabanta.

Daga nan mai shari’a Hadiza Suleiman ta dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Afrilun 2024 domin sauraren bangarorin biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *