• Wed. May 15th, 2024

Gwamnatin Kano Zata Dauki Mataki Kan Dukkan Masu Zuba Shara a Guraren Da Aka Hana

ByEditor

Apr 18, 2024

DAGA: KAMAL UMAR KURNA.

Gwamnatin jihar kano ta bayyana cewa zata dauki matakin doka akan mutanen da suke zubar da shara a wuraren da aka hana.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan lokacin daya jagoranci shugaban hukumar KAROTA Faisal Mahmud yin rangadin wuraren da aka hana zubar da sharar.

A cewar Dan Zago gwamnati ba zata lamunci halin rashin kishi da kula muhallai da wasu suke nunawa ba ta hanyar zubar da shara barkatai a jihar nan, a dan haka ne hukumar sa ta hada hannu da hukumar KAROTA domin daukar mataki akan masu zubar da shara a wuraren da aka hana.

KU KARANTA: Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Kwamishino 4, Masu Bashi Shawara 8

Da yake nasa jawabin, Shugaban hukumar KAROTA Faisal Mahmud ya ce, hukumar sa zata girke jami’anta a wuraren da gwamnati ta hana zubar da sharar domin daukar matakan da suka dace dan ganin an tsaftace jihar Kano.

Wuraren da gwamnati ta ce za’a fara dasu wajen tursasa hana zubar da sharar sun hada da Kwari ‘yan hula da jikin katangar asibitin kashi na Dala wato “Dala Orthopedic” sai gadar kasa ta kofar ruwa da saman gadar da sauran gurare da hukumar bata amince a zubar da sharar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *