• Wed. May 15th, 2024

Yakin Sudan Cikin Shekara Daya: Mutane Miliyan 18 Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa

ByEditor

Apr 18, 2024

Shekara guda kenan bayan da rikici ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF), wanda ya jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.

Rikicin dai ya faro ne a babban birnin ƙasar Khartoum amma kuma ya bazu zuwa faɗin ƙasar, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da lalata gine-gine da ababen more rayuwa.

Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa BBC cewa, a halin yanzu Sudan na kan hanyar da za ta zama ƙasar da ta fi fama da matsalar yunwa a duniya.

KU KARANTA: Najeriya ta Sake Kwashe ‘yan ƙasar Ta 126 Daga Sudan

“Muna fuskantar wani bala’i a hannunmu, kuma tsoro na shine kada ya ƙara ta’azzara,” in ji Michael Dunford, babban jami’in agajin gaggawa na Sudan a shirin samar da abinci na Majalisar dinkin duniya (WFP).

Kusan mutane miliyan 18 ke fama da ”matsananciyar yunwa” kuma wannan adadi na iya keta haka nan gaba.

Masana harkokin agaji sun kuma yi gargadin cewa mutane 220,000 za su iya mutuwa a watanni masu zuwa.

Faɗan ya ɓarke ne a ranar 15 ga Afrilun 2023 lokacin da aka raba gari tsakanin rundunar sojin ƙasar da Dakarun RSF.

Abin da ya haddasa lamarin shi ne wani shirin siyasa da ke samun goyon bayan ƙasashen duniya da ke da niyyar mayar da mulki ga fararen hula.

Wasu Alƙaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa kusan mutane 14,000 da suka mutu, to amma wasu na ganin adadin ya ninka haka.

Sama da mutane miliyan takwas (8,000,000.00) ne aka tilastawa barin gidajensu, inda da dama suka rasa matsugunansu yayin da wasu kuma suka tsallaka kan iyaka zuwa ƙasashen da ke makwabtaka da Sudan.

KU KARANTA: Za’a Kara Kudi Idan Yakin Sudan Ya Kai Lokacin Hajji – NAHCON

Birni mai tarihi ya zama kufai
Babban birnin, Khartoum, tare da garuruwan Omdurman da Bahri da ke makwabtaka da juna, su ne suka haɗa babban garin Khartoum.

Khartoum gida ne ga mutane sama da miliyan bakwai kafin yaƙin, amma yanzu ya zama kufai.

Dakarun RSF na rike da yankuna da dama na birnin amma sojojin na kai hare-hare kuma a baya-bayan nan sun ƙwace iko da hedkwatar gidan talabijin na ƙasar da ke Omdurman.

An ruguza aƙalla asibitoci uku da jami’a daya sakamakon rikicin.

A cikin watan Janairu, matatar mai ta al-Jaili da ke arewacin Khartoum ta kama wuta bayan da aka ce an gwabza faɗa.

Matatar ta kasance a tsakiyar rikicin iko tsakanin ɓangarorin da ke faɗa da juna.

Wani mai bincike a wata ƙungiyar agaji ta Burtaniya, mai lura da rikice-rikice da muhalli Leon Moreland ya ce manyan tankunan ajiya 32 sun lalace a wasu hare-hare guda uku tsakanin watan Nuwamba 2023 da Janairun 2024.

Wasu hotunan tauraron ɗan adam sun kuma nuna cewa babu komai a cikin tankunan ajiyar ruwa a tashoshin ruwa guda uku a birnin Khartoum. Ba a kuma san yadda hakan ya faru ba.

Hassan Mohammed, ɗan shekara 31 daga birnin Khartoum, ya shaida wa BBC Arabic cewa ya shafe watanni huɗu yana fama da matsalar rashin ruwan sha da wutar lantarki.

Ya ƙara da cewa “suna tafiya mai nisa don samun ruwa mai tsafta ko kuma dogaro da ruwan kogin da bai dace da sha ba, wanda ke janyo yaɗuwar cututtuka.”

KU KARANTA: Majalisar Dinkin Duniya ta Amince da Sakacinta a Yakin Sudan

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jiragen sama na Khartoum a farkon yaƙin bayan ya kasance fagen daga, wanda hakan ya yi tasiri wajen isar da kayan agaji cikin kasar.

BBC Verify ta tabbatar da wasu bidiyo daga filin jirgin saman a farkon sa’o’i 48 na rikicin kamar yadda wasu mutane suka yaɗa ta kafafen sada zumunta kamar haka:

Bidiyon farko da BBC Verify ya duba a ranar 15 ga Afrilu ya fito ne daga ɓangaren arewacin ƙarshen titin jirgin, inda aka ga dakarun RSF na gudu ta titin jirgin suna kuma harbi a kusa da manyan gine-ginen filin jirgin.

Ana kuma gwabza faɗa a wasu sassan ƙasar Sudan, musamman a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar, inda aka shafe shekaru ana tashe tashen hankula tsakanin al’ummarta na Afirka da Larabawa.

Wani bincike na baya-bayan nan da Cibiyar Yaɗa Labarai ta Resilience – wata ƙungiyar bincike da gwamnatin Birtaniya ta yi – ya gano cewa an kona ƙauyuka sama da 100 a yammacin Sudan.

Wani mai sharhi kan tattalin arzikin Sudan Wael Fahmy ya ce tasirin da yaƙin ke yi yakin ke yi a fannin tattalin arziki da kuma tsarin abinci ya yi haddasa yanayi mai matukar hadari.

“Tattalin arzikin ƙasar ya ragu da 50% kuma kusan kashi 60% na ayyukan noma ya sun tsaya,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *