• Wed. May 15th, 2024

Amurka ta ƙaƙaba Takunkumi Kan Jagororin Masu Iƙirarin Jihadi a Afrika ta Yamma

ByEditor

Apr 24, 2024

Kasar Amurka ta ƙaƙaba wa wasu jagororin ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke Afrika ta Yamma takunkumi kan garkuwa da ƴan ƙasarta.

An ɗauki takunkumin kan jagororin ƙungiya mai alaƙa da al-Qaeda ta Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin da kuma al-Murabitoun ta ƙasar Mali.

“JNIM na amfani da garkuwa da kuma tsare farar hula wajen samun abin da suke so da kuma saka tsoro inda suke sa mutanen da suka tsare da iyalansu cikin baƙin ciki da tashin hankali”, a cewar Jami’in kula da baitul mali Brian E. Nelson a wata sanarwa.

KU KARANTA: Ba Bu Amincewar Mutanen Mali, Burkina Faso, Niger a Ficewa Daga ECOWAS — Shugaban CISLAC

Ya ƙara da cewa “baitul mali zai ci gaba da amfani da ikonmu wajen tabbatar da masu garkuwa da ƴan ƙasarmu sun fuskanci hukunci”.

A sanarwar ya ce mutanen da aka ƙaƙabawa takunkumin sun taimaka da ɗaukar nauyi da kuma ba da goyon baya a garkuwa da tsare ƴan Amurka a Yammacin Afrika.

Baitul malin Amurka da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar da suka saka takunkumin sun ce “duka kadarorin da kuma kuɗin ruwan da ake biya a kan kadarorin na ƙungiyoyin da ke Amurka an hana su taba su”.

An hana ƴan Amurka yin mu’amala da mutanen da aka ƙaƙaba wa takunkumin waɗanda ƴan asalin Mali ne da Aljeriya da Burkina Faso da Mauritania.

Takunkumin yazo ne yayin da yankin Sahel na Afrika ta yamma ke yaƙi da ta’addanci daga ƙungiyoyin masu alaƙa da ƙungiyar IS da al-Qaeda.

BBC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *